

- Anyi hasashen samun ruwan sama hade da tsawa a fadin kasarnan daga yau zuwa ranar Laraba - August 23, 2021
- Wata kungiyar adawa ta ce tana da dubban mayaka da zasu fafata yaki da yan Taliban a Afghanistan - August 23, 2021
- ‘Yan bindiga sun kashe mutane 4 tare da sace wasu 50 a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara - August 23, 2021
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi kiran da a kara samun hadin kai tsakanin gwamnonin jihoshi da kwamitin shugaban kasa na karta kwana kan cutar corona.
Shugaban kasar ya sanar da hakan lokacin da yake ganawa ta bidiyon kai tsaye tare da wasu daga cikin gwamnonin Najeriya jiya Litinin.
A wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar, yace kwamitin karta kwanan yayi masa bayani akan matakan da za a dauka a gaba, wajen magance annobar a kasarnan.
Yace a dalilin haka shugaban kasar ya umarci kwamitin karta kwanan da yayi aiki tare da gwamnonin wajen ilimintar da mutane tare da daukar matakan da suka kamata wajen kare kai.
Daga cikin wadanda suka halarci zauren majalisar zartarwa inda shugaban kasar ya gana ta bidiyon kai tsaye sun hada da ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, da gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emefiele, da shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Ibrahim Gambari, da sauransu.