Kwamishinan ilimi na jihar Kano kuma shugaban kwamatin dake da alhakin mayar da Almajirai jihohin su na asali, Alhaji Sanusi Kiru, kimanin Almajirai 2000 suka cike wa’adin tsare mutane a cibiyoyin killace masu dauke da cutar 3 dake jihar, wanda kuma ake dab da mikasu zuwa jihohinsu na asali.
Kiru dai ya bayyana hakane, yayin da ya jagoranci tawagar wata kungiyar mata, da sauran wasu kungiyoyi masu zaman kansu, a ziyarar gani da ido da suka kai cibiyoyin killace masu cutar corona dake Kiru da Karaye.
Yace makasudin killace almajiran gabanin mikasu jihohinsu na asali, shine tabbatar da cewar suna cikin koshin lafiya, inda wadanda yan asalin jihar Kano ne daga cikinsu, za’a mikasu ga iyayensu.
- Jagoran juyin mulkin Gabon na yin kokarin kawo karshen takunkumin da aka kakabawa kasar
- Rikicin soyayya ya yi sandiyyar mutuwar wani matashi dan jami’a
- An kama wasu mutane 2 bisa zargin kisan wani mutum a jihar Filato
- Gwamnatin Najeriya na kokarin samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya ga ‘yan Najeriya
- Ana tuhumar mai dakin Ali Bongo da laifin karkatar da kudade da wasu laifuffuka
Kiru ya bayar da tabbacin cewa ana samar da duk wasu abubuwan bukata, musamman da ya dangaci tsaftatacciyar cimaka, da sauran kayayyakin walwala a cibiyoyin killace mutanen, domin tabbatar musu da yanayin lafiya mai inganci.

Ya kuma ce gwamnonin arewa, sun cimma matsaya kan mayar da almajiran zuwa jihohinsu ne, a matsayin rigakafin shawo kan bazuwar cutar corona.
Kwamishinan ya kuma sanar cewa, nan da kwanaki biyu zuwa uku, za’a cigaba da jigilar almajiran zuwa garuruwansu.