Mutane 71 sun Murmure sun Warke daga Korona a Jigawa

0 119

Kimanin mutane 9 ne da ke jinyar Corona gwamnatin jihar Jigawa ta bayar da sanarwar ta sallama, bayan warkewarsu daga cutar.

Shugaban kwamatin yaki da cutar a jihar kuma kwamishinan lafiya Dr. Abba Zakar ne ya sanar da hakan ga manema labarai a garin Dutse babban birnin jihar.

A baya bayannan dai sama da mutum 60 aka bayar da rahoton an sallama, bayan gwajin da akayi musu har sau 2 ya nuna basa dauke da cutar, wanda hakane ya kawo jimillar wadanda suka murmure a fadin jihar zuwa 71, inda mutum 3 sukace garinku nan.

Zakar yace kwamatin yaki da cutar ya karbi sakamakon gwajin mutane 9n daga dakin gwaje gwaje na jami’ar Bayero dake Kano, wanda ya nuna basa dauke da cutar.

Ya kuma ce tuni aka sallami mutanen, wanda ya kawo jimillar wadanda suka warke a jihar zuwa 71, daga cikin mutum 198 da aka bayar da rahoton sun kamu da cutar a fadin jihar.

Zakar yace daga cikin marasa lafiyar 198, 98 almajirai ne da aka dawo dasu daga jihohi daban daban, sai sauran mutum 100 daga sassan jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: