Babban cigaba: Gwamnonin Jihohi zasu hada kai da ta Tarayya don Cigaban Kasa

0 100

Gwamnonin kasarnan 36, sunyi alkawarin aiki tare da sabon shugaban ma’akatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari.

Cikin wasikar taya murna da kungiyar gwamnonin ta aike, mai dauke da kwanan watan 18 ga Mayun shekarar da muke ciki, dauke da sa hannun shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi, sunce hakan ya zama wajibi, musamman duba da karyewar farashin mai da cutar corona tayi sanadi.

Gwamnonin dai cikin wasikar da suka aikewa Gambari, sun bayyana farin cikinsu kan nadin nasa, duba da cancantarsa, bisa gogayya da kuma kwarewar aiki da yake da ita.

Haka kuma sunyi fatan nasara gareshi,  wajen gudanar da ayyukansa cikin yanayi dake tattare da kalubale.

Leave a Reply

%d bloggers like this: