Kano Ta Cika Da Almajiran Da Aka Kwaso Saboda Korona, yawansu ya kai 2000

0 82

Gwamnatin jihar kano ta dauki matakin killace almajirai dubu 2 a wani mataki na dakile yaduwar cutar korona a fadin jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Aminu Tsanyawa ne sanar da haka ga manema labarai jiya Alkhamin a birnin Kano.

Yayinda ake gudanar da  wata horaswa ga yan kwamatin karta kwana kan yaki da cutar covid19, yace wadanda ke aikin tantancewar almajirai ne sannan  sun hada, likitoci, maaikatan jiyya da ungozoma, maikatan lafiya, da kuma maaikatan daki gwaje-gwaje a sansanin killace masu dauke da kwayar cutar na karamar hukumar  Kiru, Gabasawa, da na karamar hukumar Karaye.

Leave a Reply

%d bloggers like this: