Matakin Da Gwamnatin Jigawa Ta Dauka Kan Masu Korona A Jihar

0 170

kwamatin kartawana kan yaki da annobar korona a jihar jigawa tace ta karbi Karin wasu mutum 28 da aka tabbatar sun kamu da kwayar cutar CORONA , wanda jimillar masu dauke da cutar a jihar ya kai mutane 169.

Shugaban kwamatin kuma kwamishinan lafiya na jiha Dr Abba Zakari ne ya sanar da haka ga manema labarai a birnin Dutse.

Yace cikin cikin mutane 169 da aka tabbatar sun kamu da kwayar cutar, kashi 97 ko 60 almajiraine da aka dawo dasu daga wasu jihohin a arewacin kasar nan.

Dr Zakari ya kara da cewa cikin samfur  23 da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa ta dawowa  jihar nan da su, 14 daga cikin mutanen sun fito ne daga birnin Dutse, 2 a Ringim sai 4 daga Birnin kudu sai kuma guda daga karamar hukumar Taura.

Ya cigaba da cewa suna cigaba da tantance wasu samfuran mutane 536 da aka kawo daga jihar Nassarawa.

A jawabinsa kwamishinan yace samfurin masu dauke da cutar guda 77 da aka killace a jihar kano zaa sake yin wani gwajin na biyu akan su , dazarar an samu gwajin ya nuna basa dauke da kwayar cutar sannan sai a sallamesu,

 Dr Abba Zakari yayi bayanin cewa gwamnatin jihar jigawa na iya bakin kokarin ta wajen samar da motocin sufuri domin daukar majinyata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: