Wani Banki Ya Bawa Jigawa Gudunmuwar Miliyoyi don yaki da Korona

0 102

Bankin Fidelity ya bayar da gudunmawar kudi naira miliyan 5 ga gwamnatin jihar Jigawa domin agazawa yaki da bazuwar cutar corona a jiharnan.

Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar wanda ya karbi gudunmawar ya yabawa kokarin bankin wajen kula da al’umma, inda ya bukaci sauran kamfanoni da masu hannu da shuni, su yi koyi da karamcin.

A wani labarin kuma, wata kungiya mai zaman kanta mai kula da ‘yan gudun hijira a nan jihar Jigawa, ta bayar da gudunmawar katan 20 na sabulu domin agazawa yaki da annobar corona a jihar nan.

Daraktan kungiyar, Muhammad Sulaiman, shine ya gabatar da gudunmawar ga dan kwamitin karta kwana, Musbahu Basirka, a sansanin horas da matasa masu yiwa kasa hidima NYSC dake Fanisau.

Yace sun bayar da gudunmawar da nufin tallafawa kokarin gwamnatin jihar wajen yaki da annobar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: