Tallafin Miliyan 19 ta shiga hannun kwamitin yaki da Korona a Jigawa

0 164

A wani cigaban makamancin wannan kuma, kamfanin gine-gine na Ganan ya bayar da gudunmawar kayan aiki na naira miliyan 19 ga kwamitin karta kwana na jihar Jigawa kan cutar corona.

Manajin Darakta na kamfanin, Mista Ganan, shine ya mika kayan ga kwamishinan lafiya na jiha a Dutse.

Yace sun bayar da gudunmawar da nufin tallafawa kokarin gwamnatin jihar wajen yaki da annobar.

Da yake karbar gudunmawar, kwamishinan lafiya wanda kuma shine shugaban kwamitin karta kwana kan cutar corona, Dr Abba Zakari Umar, ya yabawa kamfanin bisa karamcin.

Dr. Abba Zakari yace gidanauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello Sardauna ta bayar da gudunmawar takunkumin rufe fuska guda 1,500 ga kwamitin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: