Za’a Gudanar da Sallar Idi a Jigawa kamar yadda aka saba

0 133

Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya amince da a gudanar da sallar Idi kamar yadda aka saba amma bisa sharadin shawarar cewa Mata da ƙananan yara da kuma tsofaffi ba zasu halarta ba saboda raunin garkuwar jikinsu.

Domin kiyaye su daga kamuwa da duk wata cuta da ka iya zama barazana ga rayuwar su.

Gwamnan yayi wannan albishir din ne na yiwuwar sallar Idi yayin da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar Jigawa dake Dutse.

Sai dai ya ce ya zama wajibi a bi shawarar likitoci ta bayar da tazara a tsakanin masu gudanar da sallar tare kuma da sanya ta chanhu ko takunkumin kare hanci da baki (Face Mask) kafin a kyale mutum ya shiga filin irin.

Amma kuma da zarar an gudanar da sallar idin duk wuraren da aka Sanya dokar kulle bayan sallar da karfe 12:00pm zasu cigaba da zaman gida (babu yawon sallah washegari).

Duk wani hawan sallah ko shagali ko kuma biki an soke shi (saboda halin da ake ciki).

Haka zalika gwamna Badaru ya sake tsawaita zaman gida ga ma’aikatan gwamnati na jihar da ƙarin makonni biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: