Dole duk mai son zuwa Sallar idi ya sanya takunkumin rufe baki da hanci a Jigawa

0 143

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce daga yanzu ya zama dole ga masu zuwa sallar Idi su sanya takunkumin rufe baki da hanci a fadin Jihar nan.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bada wannan umarni a taron manema labarai da ya gudanar a gidan Gwamnati dake Dutse.

Ya ce an hana tsoffi da kananan yara zuwa sallar idin, yayin da za a tabbatar da tazara a tsakanin juna da kuma amfani da takunkumin rufe baki da hanci a lokacin sallar.

Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya kara da cewa za a fara sallar idin da misalin karfe takwas na safe, yayin da aka umarci limamai su gabatar da takaitacciyar huduba.

Gwamnan ya yi bayanin cewa Gwamnati ta soke dukkanin bukukuwan karamar sallar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: