An soke hawan Sallah a Bauchi

0 42

Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaiman, ya soke hawan Daushe, wanda ake gudanarwa kwana daya bayan Sallah a Bauchi.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa hawan dawakan wani bikin ne da sarakunan Arewa ke shiryawa, wanda yake jawo hankalin dubban mutane lokacin bukukuwan Sallah.

Rilwanu Sulaiman ya fada a taron ganawar masu ruwa da tsaki, tare da gwamnatin jihar Bauchi cewa soke hawan ya zama tilas sanadiyyar annobar corona a fadin duniya.

Yace duniya na fama da cutar corona wacce ta jawo wahalhalu marasa adadi ga mutane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: