An shirya wani taron karawa juna sani ga ‘yan kasuwa 510 a jihar Kebbi

0 204

Kungiyar ‘Yan Kasuwa ta kasa reshen jihar Kebbi, ta shirya wani taron karawa juna sani ga ‘yan kasuwa 510 a jihar.

Da yake jawabi a wajen rantsar da mambobin kungiyar na jiha a Birnin Kebbi a jiya litinin, Gwamna Nasir Idris ya yi alkawarin taimakawa kungiyar domin cimma manufofinta.

Gwamnan ya yabawa kungiyar bisa hazakar da ta yi, sannan ya bukace ta da ta ci gaba da samar tsari mai kyau domin amfanin sauran mambobin kungiyar.

Tun da farko a jawabin bude taro, kwamishinan kasuwanci na jihar Kebbi, Alhaji Usman Ladan-Dakingari, ya yabawa gwamnan bisa yadda yake tallafawa kungiyar. Ya kuma ja hankalin sabbin shugabannin kungiyar da su mai da hankali kan abin da zai kawo hadin kai a tsakanin mambobin ta da kuma ci gaban jihar Kebbi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: