An kaddamar da sabbin shugabannin kungiyar Muryar Birnin kudu

0 197

An kaddamar sabbin Yan kwamatin amintattu da Yan kwamatin koli da kuma shugabannin kungiyar Muryar Birnin kudu a lokacin taron kungiyar na shekara shekara da aka gudanar a kwalejin aikin jiyya da Ungozoma da ke Birnin Kudu.

Wadanda aka kaddamar sun hadar da Hakimin Birnin Kudu , Alhaji Garba Hassan Jibrin a matsayin  shugaban kwamatin aminatattu da Alhaji Adamu Mu’azu shugaban kwamatin koli yayinda Alhaji Balarabe Sa’id Jarman Birnin kudu aka nada a matsayin shugaban kungiyar.

A jawabinsa na kaddamarwa, Galadiman Dutse Alhaji Basiru Muhammad Sanusi ya yi addu’ar Allah Ya ba su ikon sauke nauyin da ke kan su.

A jawabaninsa na maraba, shugaban kungiyar mai barin gado kuma Hakimin Birnin Kudu Alhaji Garba Hassan Jibrin, ya ce kungiyar ba ta siyasa ko jayayya da gwamnati ba ce sai dan lalubo hanyoyin da za su taimaka wajen kawo cigaban yankin.

A nasa jawabin, shugaban taro kuma sakataren gwamnatin jihar Jigawa Malam Bala Ibrahim MAMSA, ya yi addu’ar Allah madaukakin Sarki Ya karfafi ayyukan kungiyar a kokarinta na jagorantar sauran kungiyoyin kyautata jin dadin jama’a wajen cigaban yankin.

A lokacin taron, kungiyar ta karrama wasu mutane da kamfanoni da suka yi fice wajen kawo cigaban al’umma da suka hadar da Hakimin Birnin Kudu Alhaji Garba Hassan Jibrin da mataimakin kwamishinan yan sanda ACP Sanusi Aliyu da sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na kasa kuma babban lauya a Najeriya Musa Asamu Aliyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: