An tabbatar da mutuwar mutane 6 a wani hatsarin mota sanadiyyar aikin hanya da ake yi

0 267

Hukumar kula da hanyoyi ta kasa a Jihar Zamfara, ta tabbatar da mutuwar mutane 6 a wani hatsarin da a garin Gusau, sanadiyyar aikin hanya da ake yi a jihar.

Kwamandan hukumar na Jihar Zamfara Iro Danladi, shine ya sanar da haka a jiya, yana mai cewa ya kamata al’umma su lura da aikin da ake yi a garin.

Yace a wannan lokaci da ake aikin gina hanyoyin a Gusau babban Birnin Jihar, akalla mutane shida ne suka nutu a hatsarin mota daban-daban.

Wadanda hatsarin ya rutsa da su galibi Mata ne da kananan yara masu tsallaka hanya.

A cewar Iro Danladi, duk da akwai jami’an hukumar kula da hanya ta kasa domin lura da ababan hawa,akwai bukatar kamfanonin dake aiki a wuraran su samar da alamomin da su janyo hankali matafiya da sauran jama’a dake nuna ana aiki a wurin domin kaucewa faruwar haddura. Kazalika, yayi kira ga gwamnati ta wayar da kan jama’a yadda zasu yi amfani da hanyoyin a lokutan da ake yin aiki, la’akari da rin kalubalan da ake fuskanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: