An yiwa ma’aikata 2005 karin girma a cikin kwanaki dari na gwamna Mallam Umar Namadi

0 221

Hukumar lura da ma’aikatan kananan hukumomi ta jihar Jigawa tace a cikin kwanaki dari na gwamna Mallam Umar Namadi ta yiwa ma’aikata dubu biyu da biyar Karin girma.

Shugaban Hukumar, Alhaji Uba Bala Ringim ya sanar da hakan yau a Dutse babban birnin jiha.

Yace ma’aikatan sun kunshi na kananan hukumomin jiha 27.

Uba Bala Ringim yace sun biya kudi naira miliyan biyu da dubu dari biyar a matsayin tallafin karatu ga ma’aikatan kananan hukumomi dake karatu a manyan makarantun ciki da  wajen jihar nan

A cewarsa sun gudanar da taron bitar sau 100 ga rukunin maa’ikatan kananan hukumomi, yayinda suka gudanar da taron karawa juna sani har sau 25 a ciki da wajen jihar nan ga rukunin maaikatan hukumar Ya bada tabbacin hukumar na cigaba da kula da jin dadin maaikatan kananan hukumomi, tare da basu shawarar zuwa wuraren aiyukansu akan lokaci

Leave a Reply

%d bloggers like this: