Dakarun sa kai na RSF a Sudan sun kwace Filin Jirgin sama da sojojin kasar ke amfani da shi,sunce zasu janye daga yanki saboda hare-hare da ake kai musu suk da kokarin da Saudiya ke yi na shiga tsakani.
Dakarun na RSF sun ce filin Jirgin saman na Belila dake yammacin Jihar Kordofan da sojojin kasar ke amfani da shi, tun lokacin da aka fara yaki a tsakiyar watan Afrilu.
Bangarorin biyu na fafatawa da juna a Birnan El Obeid da El Fasher a yan kwanakin nan, a daid-dai lokacin kasashen Amurka da Saudiya ke tattaunawa a Birnin Jedda domin a tsagaiwata wuta. A jiya kungiyar bada agaji ta Red Cross ta taimakawa wajen sako sojojin sudan 64, adadin da yakai sojojin Sudan da aka sako ya kai 292 tun fara yakin a kasar.