Mutane 13 ne suka rasu sanadiyyar wasu jiragen kasa da suka yi taho mu gama a kasar India

0 177

Lamarin ya farune a karshen makon da ya gatana a tsakanin garuruwan Alamanda da Kantakapalle dake jihar Pradesh.

Hukumomin a yankin sunce Fasinjoji 13 suka mutu wasu 50 suka ji munanan raunuka, yayinda ake cigaba da aikin ceto.

Firamistan India Narendra Modi yayi magana da Ministan sufurin jiragen kasa na kasar domin ya dauki mataki kan wannan lamari.

Hatsarin jirgin kasa yayi sanadiyyar mutuwar 800 a kasar India yan kwanakin nan.

Kasar tana daya daga cikin kasashen duniya dake amfani da layukan dogo wajen tafiye-tafiye na fuskantar hatsarin jiragen kasa a ‘Yan shekarun nan.

A watan Yuni, wasu jiragen kasa uku sunyi taho mu gama a Jihar Odisha lamarin da yayi sanadiyyar mutuwa mutane kusan 300.

A watan Agsuta ma wasu mutane 9 sun mutu a kudancin kasar. A farkon watan nan ma wasu mutane 4 sun Mutu a tashar jirgin kasa dake Bihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: