Dukkanin wani minista zai ci gaba da rike ofishinsa ne kawai bisa la’akari da ayyukan da yayi

0 200

Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke bude taron majalisar ministoci da masu taimaka wa shugaban kasa da kuma manyan sakatarorin ma’aikatu na shekarar 2023, wanda aka gudana a Abuja.

Taron wanda aka yiwa take da cimma Muradin sabunta fata ga yan Najeriya, shugaban ya tunasar da ministocin ayyukan da ke gabansu na sauke nauyin al’ummar da ke wuyansu

Ya kuma bukaci ministocin su maida hankali wajen samar da ci gaba a ma’aikatun da suke jagoranta, inda ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ganin ta kasance kan gaba wajen ci gaba.

Dukkanin ministoci, sun samu halartar taron na kwanaki uku, in banda ministan yawon shakatawa Mrs Lola Ade-John. Tinubu ya kuma jaddada bukatar samar da sakamako mai kyau ga yan Najeriya musamman a bangarorin da aka fi bawa fifiko, da suka hada da kiwon lafiya da fannin ilimi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: