Shugaba Tinubu na shirin karbo bashin $7.8Bn da kuma £100M

0 221

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya nemi amincewar majalisar dattijai domin shirin karbo bashin dala biliyan 7.8 da kuma euro miliyan 100 a bashin waje na 2022-2024.

Shugaban kasar ya mika bukatar ne ta cikin wata takarda da shugaban majalisar Godswill Akpabio ya karanta a zauran majalisar jiya.

Cikin takardar Shugaban kasar yace gwamnatin data gabata ta amince da karbo bashi tsakanin shekarun 2022-2024 a wani zaman majalisaar zartaswa a ranar 15 ga watan Mayu.

Shugaba Tinubu yace za’ayi amfani da kudaden a dukkan bangarori musamman fannin gine-gine, aikin gona, kiwon lafiya, ilimi, samar da ruwa, tsaro da samar da ayyukan yi domin bunkasa tattalin arzikin kasa.

Haka kuma majalisar ta amince da bukatar shugaban kasar na karbo bashin dala biliyan 7.8 da kuma euro miliyan 100. Majalisar ta kuma amince da nadin kwamishinonin zabe 7 da shugaban kasar ya aike dasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: