Yan Najeriya 99 da suka makale a Jamhuriyar Nijar aka dawo dasu gida Najeriya a Jiya

0 55

An sauke su ne a Filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa na Murtala Muhammad karkashin shirin hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya.

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ce ta karbi su a madadin gwamnatin Tarayya.

An samu rashin jituwa a wasu kasashen Yammacin Afrika tun bayan juyin Mulkin sojoji a Nijar.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta matsawa gwamnatin Nijar lamba domin maida mulkin farar hula a Nijar. Wadanda aka dawo da su sun hada da mata 15 ciki hadda wasu likitoci 2, da kuma maza 60, sai ‘yan mata 7, samari 15 sauran sun hada da jarirai 2.

Leave a Reply

%d bloggers like this: