Hukumar raya yankin Arewa Maso Gabas ta bada gudunmawar N2Bn ga yan kasuwar Maiduguri

0 193

Hukumar raya yankin Arewa Maso Gabas, ta bada gudunmawar Naira Bilyan 2 ga yan kasuwar Maiduguri da aka sake bude ta bayan ta kama da wuta a watan Fabareru.

Manajin Daraktan Hukumar Muhammad Alkali, shine ya sanar da bada wannan tallafin a Maiduguri yayin wata ziyarar ban girma da yakaiwa Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar.

Muhammad Alkali ya yabawa gwamnan Jihar bisa yadda ya gyra kasuwar cikin kankanin lokaci.

Ya kara da cewa hukumar raya yankin Arewa Maso Gabas zata tallafawa yan kasuwa da kayayyakin su suka kone a kasuwar ta Maiduguri.

Gwamnan wanda yabawa hukumar, ya kuma bukaci ta samar da hanyoyi, ilimi,wutar lantarki da kayan noma ga mazauna yankunan. Ya kuma nemi gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu, da ta taimakawa wajen raya yankin Arewa Maso gabashin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: