Najeriya zata kai ga hakar ganga Milyan 1.8 a kowacce rana

0 158

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio yace sannu a hankali Najeriya zata kai ga tsarin kungiyar kasashe masu arzikin Man Fetur ta OPEC na hakar ganga Milyan 1.8 a kowacce rana.

Godswill Akpabio,ya fadi haka ne yayin wani taron bita da kungiyar masu kasuwanci da samar da Man Fetur ta shirya jiya a Abuja.

Ya bayyana jin dadin sa bisa yadda ake hako gangar mai Milyan 1.35 kowacce rana a watan Satumba.

Yayi fatan cewa gwamnatin tarayya da kamfanonin samar da Man Fetur zasu taimakawa Najeriya wajan samar da cigaba mai dorewa a harkar hako man fetur. Shugaban Majalisar Dattawan yace wannan dalili ne yasa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu yasa ta janye tallafin Man Fetur, dake yin illa ga tattalin arzikin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: