Ana zargin matar aure da kashe ’yar kishiyarta mai shekara 3
’Yan sanda sun kama wata matar aure kan zargin kashe ’yar kishiyarta mai shekara uku ta hanyar shaƙe ta har lahira a yankin Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara.
A cewar rundunar, wadda ake zargin ta kashe yarinyar ne saboda zafin kishi, saboda cewarta, mijinta ya yi watsi da ita da ’ya’yansu uku, inda ya fifita matarsa amaryarsa.
’Yan sandan sun ce wadda ake zargin ta yaudari yarinyar ta fita daga gidansu zuwa wata gona da ke kusa, inda ake zargin ta kashe ta bayan wata doguwar taƙaddamar iyali.
Da take ƙarin bayani kan lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce lamarin ya faru ne ranar 25 ga Yuli, bayan mahaifiyar yarinyar ta bar ta a hannun wani ɗan uwa yayin da ta je Kasuwar Tsakiyar Kaiama.
A cewar rundunar, wadda ake zargin ta ɗauki yarinyar daga gida zuwa wata gona, inda ta shake ta.
Ejire-Adeyemi ta ce jami’an bincike na Hedikwatar ’Yan Sandan Kaiama sun fara bincike nan take, wanda ya kai ga kama wadda ake zargin.
Ta ce yayin da ake yi mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa laifin, inda ta shaida wa masu bincike cewa fushi da kishi ne suka sa ta aikata abin, sakamakon wata doguwar taƙaddamar cikin gida.
Kakakin ’yan sandan ta ce an kammala binciken lamarin, kuma an gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar shari’a.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su riƙa yin taka-tsantsan tare da gaggauta bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen hana aikata laifuka da kama masu hannu a su.