’Yan Bindiga Sun Sace Mai Shekara 90 A Neja

0 30

’Yan bindiga sun sace mai shekara 90 a Neja

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dattijo mai shekaru 90, Malam Abubakar Lafiya, a yankin Ka’ada da ke gundumar Dekara, Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja.

Majiyoyi sun shaida wa wakilanmu cewa da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Asabar ne ’yan bindigar suka kai farmaki gidan dattijon, wanda shi ne mai unguwar ƙauyen, inda suka yi ta harbe-harbe kafin su yi awon gaba da shi.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa mai unguwar da aka sace shi ne mahaifin Hakimin Dekara na yanzu.

Ya ce sace dattijon ya jefa al’ummar Ka’ada, Dekara da sauran ƙauyukan da ke maƙwabtaka da su cikin fargaba, musamman saboda la’akari tsufansa.

“Lamarin ya jefa mu cikin damuwa, musamman ganin cewa mai unguwar ya kai shekara 90 a duniya,” in ji shi.

Ya bayyana sace dattijon a matsayin abin takaici da tashin hankali, yana mai cewa al’ummar yankin na ci gaba da addu’o’in Allah Ya dawo da shi lafiya.

Mazauna yankin sun kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar matakin ceto shi tare da tabbatar da tsaron lafiyarsa.

Ƙoƙarin jin ta bakin ’yan sanda kan lamarin bai yi nasara ba, domin ba a samu damar tuntuɓar mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

Leave a Reply