Anyi hasashen karancin ruwan sama a daminar bana mai kamawa

0 114

Ga manoma a jihoshi 7 na kasarnan, hasashen ruwan sama na bana ya nuna sakamako mara kyau kasancewar zasu iya asarar shukarsu a tsakiyar damuna.

Hukumar hasashen yanayi ta kasa a makon da ya gabata ta saki hasashenta na ruwan saman na shekara-shekara, daidai lokacin da manoma ke shirin fara shuka a gonaki.

Rahoton hasashen ya nuna cewa daga watan Mayu zuwa Yunin bana, akwai yiwuwar samun babban fari da zai kwashe kwanaki 15 zuwa 20 a mafiya yawan jihoshin Arewa, yayin da za a samu karamin fari daga watan Yuli zuwa Augusta.

Manoma a sassan jihoshin Jigawa, Yobe, Katsina, Borno, Kebbi, Filato da Nasarawa zasu fuskanci mummunan fari a watan Yunin bana, daidai lokacin da amfanin gona ke bukatar ruwan sama sosai.

A jihar Jigawa, anyi hasashen samun farin a kananan hukumomin in Gwiwa, Yankwashi, Gumel, Sule-Tankarkar, Guri da kuma Kiri Kasama, yayin da a jihar Yobe lamarin zai shafi Nguru, Yusufari, Yunusari, Karasuwa, Barde, Jakusko da kuma Geidam.

Leave a Reply

%d bloggers like this: