Gwamnatin Tarayya tana shirin kashe naira tiriliyan 3 da biliyan 530 akan gine-gine tare da inganta rayuwar al’umma

0 90

Gwamnatin Tarayya tace tana shirin kashe naira tiriliyan 1 da biliyan 420 akan gine-gine tare da naira tiriliyan 2 da biliyan 110 wajen inganta rayuwar bil’adama a shekarar 2022 kadai.

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, ta sanar da haka yayin wani wani da aka shirya akan nasarorin gwamnatin tarayya a bangaren gine-gine, wanda ma’aikatar labarai da al’adu ta shirya a Abuja.

Tace gwamnati mai ci ta jajirce domin bayar da muhimmanci wajen kashe kudade a bangaren gine-gine da inganta rayuwar dan adam wanda zasu kawo cigaba sosai ga tattalin arziki, a saboda haka ta kara yawan kudaden kasafin kudi da aka warewa bangarorin.

Ministar, wacce ta yabawa takwaranta na labarai bisa hada taron, tace gwamnati mai ci ta samu nasarar aiwatar da ayyukan gine-gine da dama, wadanda suka shafi rayuwar ‘yan kasa, duk da tarun kalubalen da kasarnan ke fuskanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: