APC a Kano ta yi kira ga ‘ya’yanta da su kasance masu bin doka da oda.

0 176

A halin da ake ciki kuma, jam’iyyar APC a jihar Kano ta yi kira ga ‘ya’yanta da magoya bayanta da su kasance masu bin doka da oda.

Kwamishinan labarai da harkokin cikin gida na jihar, Muhammad Garba, shine yayi rokon cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Kano.

Kwamishinan yace jam’iyyar za ta yi duk mai yiwuwa bisa tanadin doka da matakan da aka tsara wajen tabbatar da cewa an samu adalchi dangane da batun. Muhammad Garba yace gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da mataimakinsa kuma dan takarar gwamnan jihar na APC, Nasiru Yusuf Gawuna, da abokin takararsa na mataimaki, Murtala Sule Garo, sun bayyana amincewa da halayyar ‘ya’yan jam’iyyar kafin da lokacin da kuma bayan zaben.

Leave a Reply

%d bloggers like this: