Nigeria tare da hadin gwiwar MDD ta kwashe ‘yan Najeriya 151 da suka makale a Libya.

0 65

Gwamnatin tarayya, tare da hadin gwiwar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, a jiya ta kwashe ‘yan Najeriya 151 da suka makale a birnin Benghazi na kasar Libya, daidai lokacin da gwamnati ta dawo da kwaso ‘yan gudun hijirar bisa radin kansu daga Libya.

Shugaban ofishin jakadancin Najeriya a kasar Libya, Ambassada Kabiru Musa, shine ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja.

A cewar Kabiru Musa, wadanda aka kwaso sun hada da mata 71 da maza 54 da yara 14 da jarirai 13 kuma ana sa ran saukarsu a filin jiragen saman kasa da kasa na Murtala Mohammed dake Lagos da misalin karfe 8 na dare.

Kabiru Musa yace a shekarar 2022, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya da ma’aikatar harkokin waje karkashin ofishin jakadancin Najeriya a Libya, sun samun nasarar dawo da ‘yan Najeriya dake gudun hijira ba bisa ka’ida ba a kasar su kimanin dubu 4. Yace aikin kwaso ‘yan gudun hijirar bisa radin kansu na jiya shine na farko a bana, inda za ayi makamantan hakan cikin kwanaki da makonni masu zuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: