APC Ta Bayyana Fara Sayar da Form Din Takarar Kujerun Jam’iyyarta

0 251

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta sanar da fara sayar da form din nuna sha’awa a fadin kasar nan gabanin babban zaben 2027.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin jam’iyyar na X ranar Talata. Sanarwar ta bayyana cewa mata, matasa da masu nakasa da ke neman takara za su biya kudin form din nuna sha’awa tare da rabin kudin form din tsayawa takara na kowace kujera.

Ta kuma ce tsarin rabon mukamai na Kwamitin Ayyuka na Kasa (NWC) da ake da shi a jihohi da yankunan kasa zai ci gaba da aiki, yayin da za a gudanar da tarukan zaben shugabanni na jihohi da na sanatoci a lokaci guda da tarukan jihohi.

Sanarwar ta kara da cewa jihohin Ekiti, Osun, Rivers da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT) ba za su shiga tarukan zaben gunduma, kananan hukumomi da jihohi ba. Sai dai za su halarci zaben wakilai uku zuwa babban taron kasa.

Haka kuma, cike form din za a yi ne ta yanar gizo, kuma za a ba da damar samun fom din nuna sha’awa da na tsayawa takara ne bayan an tabbatar da biyan kudi tare da sahalewar Sakatariyar Kasa. Jam’iyyar ta jaddada cewa dole ne a biya dukkan kudade kai tsaye zuwa asusun bankin da APC ta tanada.

Leave a Reply