ASUU ta koka kan matakin gwamnatin tarayyya na rushe majalisar gudanarwa a jami’o’in Najeriya

0 403

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) a jiya ta yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na rusa majalisar gudanarwa a jami’o’in kasar nan.

Kungiyar ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya janye matakin da suka bayyana a matsayin yanke shawara na rusa majalisar ba tare da kammala wa’adinsu ba.

Mataimakin shugaban kungiyar ASUU na kasa, Kwamared Christopher Piwuna, na jami’ar Jos ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da kasida a wani taron karrama malaman da suka yi ritaya a jami’ar Joseph Sarwuaan Tarka ta Makurdi (JOSTUM), wacce a da ake kira Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya. Makurdi (FUAM), a jihar Benue.

Christopher Piwuna ya ce, ba daidai ba ne a rusa majalisun gwamnati tare da mika wa ma’aikatar ilimi ta tarayya ko kuma hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) madafun iko ba tare da bin dokokin jami’a ba.

Har ila yau, hani ne ga jami’o’i su bari a tada zaune tsaye domin miyagu mataimakan shugabannin jami’o’in da jami’an ma’aikatar za su iya hada kai su ruguza jami’o’inmu idan ba a duba irin wannan rashin kula da dokokin da aka kafa jami’o’in ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: