Wata kungiya ta yan kishin kasa ta soki matakin tura sojoji zuwa jamhuriyar Nijar

0 312

Wata kungiya ta yan kishin kasa ta soki matakin tura sojoji zuwa jamhuriyar Nijar domin maido da mulkin farar hula.

Kubgiyar ECOWAS ta umarci kwamitin manyan hafsoshin tsaro na kungiyar data gaggauta amfani da karfi tuwo kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.

Wannann matakin na zuwa ne bayan da majalisar dattawa ta ki amince da matakin shugaban kasa Bola Tinubu na turo sojoji zuwa Nijar su dawo da mulkin farar hula.

Kazalika yan awanni kenan da jagororin juyin mulki suka yi barazanar kasashe shugaban Nijar Bozoum, idan kasashe makwabtaka suka kokarin shiga domin dawo da shugaban kasar da aka kifar da gwamnatin sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: