Auren dole yasa an sallami Hakimi a jihar Neja

0 112

Masarautar Minna ta dakatar da Hakimin Allawa da ke karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja, Malam Bello Haruna, kan auren dole da kuma wani aiki na rashin biyayya.

Masarautar a cikin wata wasika da mataimakin sakatarenta Usman Umaru Guni ya aikewa da wakilinmu, ta ce sarkin ya auri wata yarinya da karfi da yaji, inda ya wulakanta mahaifinta sannan kuma ya umurci ’yan banga da duka.

An kuma zargi Hakimin gundumar da rashin biyayya ga rashin amsa kiran da fadar ta yi masa na bayyana wasu korafe-korafen da ake yi masa.

Sarkin ya ce dabi’un basaraken sun nuna shi a matsayin rashin halayen jagoranci domin zaman lafiya da ci gaban al’ummar da aka nada shi.

Sai dai masarautar ta bayyana Galadima Allawa, Ahmadu Magaji a matsayin hakimin riko.

Leave a Reply

%d bloggers like this: