Majalisar zartarwa ta tarayya za fa kashe Naira biliyan 1.4 don siyan kayan aikin noma don ceto Najeriya daga fadawa yunwa

0 112

Majalisar zartaswa ta tarayya FEC ta amince da kashe Naira biliyan 1.4 don siyan kayan aiki da kayan noma don shirin manoma na kasa.

Lai Mohammed, ministan yada labarai da al’adu, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa, bayan taron FEC da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a ranar Laraba a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ya ce an bayar da kwangiloli guda hudu na shirin, ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa ayyukan za su karfafa gwiwar matasa su shiga harkar noma.

A cewarsa, na farko shi ne samar da kayan amfanin gona irin su irin auduga, kayan shuka, sinadarai na noma, taki, da shirin inganta noma, wanda zai kai hekta 3000 a Abia, Adamawa, Borno, Ekiti, Gombe, Imo, Jigawa, Katsina. Jihohin Kebbi, Niger, Osun, Yobe and Enugu.

Ya ce kwangilar farko ta Naira miliyan 313 ne na tsawon makonni biyu.

Ya ce na biyun shi ne samar da taraktoci da da manyan injunan aiki da tirelolin ruwa da jigilar kayayyaki zuwa jihohin Kaduna da Katsina da Kebbi da Osun da kuma Jigawa.

Mista Mohammed ya ce dalar shinkafa da shugaban kasa ya kaddamar kwanan nan da kuma shirin Anchor Borrowers’ ya dogara ne a kan kananan manoma maimakon manyan kamfanoni, akalla kananan manoman miliyan uku ne suka bada hadin Kwarin guiwa a yayin bikin kaddamar da dalar a Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: