‘Ba zamu kara karbar allurar rigakafin Corona mai karamin wa’adin karewa ba – Gwamnatin Najeriya

0 77

Shugabar Hukumar Lura da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce hukumar tana aiki tukuru tare da sauran kasashen Duniya domin tabbatar da cewa an kawo Najeriya rigakafin Corona mai dogon wa’adin karewa.

Mojisola, ta yi wannan jawabin ne domin mayar da martani kan rigakafin Corona Miliyan 1 da suka lalace a watan Nuwamba, wanda hukumar Lafiya a matakin Farko ta Kasa da Hukumar NAFDAC da kuma Hukumar Tsaftar Muhalli ta Abuja suka lalata.

Kamfanin Dillancin Labarin na Kasa NAN, ya rawaito cewa kimanin rigakafin Miliyan 1 da Dubu 66 ne samfurin AstraZeneca, aka lalata a yankin Gosa dake Abuja.

Mojisola Adeyeye, ta fadawa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa cewa rigakafin da suka lalace dama Karamin wa’adi ne da su, wanda kuma abu ne mai wahala a iya rabasu kafin karewar wa’adin su.

Kazalika, ta shawarci yan Najeriya su kasance masu yin taka tsantsan wajen kare kansu daga kamuwa da cutar Corona.

Leave a Reply

%d bloggers like this: