An kori wani ɗan sanda daga aiki saboda ya dauki hoton salfi a wurin da aka yi kisa

0 120

An kori wani ɗan sanda daga aiki bayan ya ɗauki hoton salfi a wurin da aka kashe wata matashiya a yankin Liverpool na Birtaniya.

PC Ryan Connolly da ke aiki da Rundunar ‘Yan sanda ta Merseyside ya kuma wallafa hotunan ƙiyayya da wariya sannan ya ɗauki hotunan wasu masu taɓin hankali ana yi musu kalaman wariya.

Rundunar ‘Yan Sanda ta Merseyside ta ce an kori mutumin mai shekara 37 saboda rashin ɗa’a biyo bayan wani binciken kwamatin yaƙi da rashawa.

Rundunar ta gano wasu hotuna masu “nuna wariya sosai” da aka ɗauka daga 2015 zuwa 2018, a cewarta.

Za a yanke masa hukunci a Kotun Manchester Crown ranar 10 ga watan Janairu mai zuwa. An taɓa kama shi da laifin amfani da komfutar ‘yan sanda ba bisa ƙa’ida ba da kuma rashin ɗa’a a bainar jama’a.

BBCHausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: