Mutum 599 sun sake harbuwa da cutar Corona a Najeriya

0 98

An samu mutane 599 da suka harbu da cutar Corona a kasar nan cikin awanni 24 da suka gabata.

Cibiyar Dakile Yaduwar Cutuka ta Kasa NCDC ita ce ta sanar da hakan, inda ta ce mutanen sun fito ne daga Jihohin 14 da suke Najeriya ciki harda birnin tarayya Abuja.

Cibiyar ta NCDC ta ce an samu mutane 194 da suka harbu da cutar a Jihar Delta, sai Edo mai mutane 94 da kuma birnin tarayya Abuja mai mutane 80.

Sauran Jihohin sune Kaduna (48), Lagos (35), Ondo (23), Kano (21), Rivers (20), Kwara (20), Ogun (18), Plateau (12), Abia (8), Cross River (8), Ekiti (6), and Bauchi (3).

NCDC ta ce a jiya an sallami mutane 410 da suka warke daga cutar wanda hakan ne yake nuni da cewa kawo yanzu an sallami mutane dubu 213 da 180 da suke warke daga cutar.

Haka kuma an bada rahotan cewa kimanin mutane 3 ne cutar ta hakkala a jiya wanda hakan ne ya kawo adadin mutane dubu 3,027 wanda Corona ta hallaka.

Kawo yanzu kimanin mutane dubu 239 da 019 ne suka warke daga cutar Corona a Jihohi 36 da suke Najeriya ciki harda birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: