Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu ya warke daga cutar Corona

0 22

Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu ya warke daga cutar Corona.

Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook a yau, bayan shafe kimanin kwanaki 7 yana dauke da cutar, kamar yadda Channels Tv ta gano hakan.

Gidan Talabijin na Channels Tv ya rawaito cewa wasu hadiman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, sun killace kansu bayan sun nuna alamun kawuwa da cutar Corona.

Duk da cewa ba’a tabbatar da adadin Hadimin Shugaban Kasar da suka kamu da cutar Coronan ba, amma Garba Shehu ya ce gwajin da aka masa ya nuna cewa ya harbu da cutar.

A cewar Garba Shehu, duk da cewa an yi masa rigakafin cutar, amma gwaje-gwajen da aka masa sun nuna cewa ya kamu da cutar Corona. Shima a Jawabinsa, Mai taimakawa Shugaban Kasa kan Kafafen Yada Labarai Mista Femi Adesina, ya ce babu wani abun mamaki dan hadiman shugaban kasa sun kamu da cutar Corona.

Leave a Reply

%d bloggers like this: