Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ce man fetur da ma sauran albarkatun kasar Najeriya na dukkan ‘yan Najeriya ne ba iya Neja Delta ba

0 94

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ce man fetur da ma sauran Albarkatun kasar na dukkan ‘yan Najeriya ne.

Ya bayyana haka ne a wani martani da ya mayar wa fitaccen dattijon nan na yankin Naija Delta, Cif Edwin Clark, wanda ya zargi Obasanjo da nuna halin ko-in-kula game da illolin da hakar mai a yankin nasu ta haddasa.

Wasu rahotanni sun ambato Clark, a cikin wata wasika da ya rubuta, yana zargin tsohon shugaban kasar da nuna kiyayya ga masu fafutukar mallakar albarkatun kasar da aka samu a yankunansu.

Sai dai a martanin da ya mayar, Obasanjo ya ce a iya saninsa albarkatun kasar da aka hako a Najeriya mallakin dukkan ‘yan kasar ne ba na mutanen yankunan da aka same su ba.

Ya kara da cewa ba zai yiwu a samu kasashe biyu a cikin kasa daya ba, yana mai cewa a iya fahimtarsa Cif Clark yana magana ne a kan samar da wata kasa a cikin Najeriya idan har yana so a ba Naija Delta damar mallakar albarkatun kasar da aka samu a yankin.

Tsohon shugaban kasar ya ce dukkan mutanen da suka kulla yarjejeniyar sayen danyen man fetur sun yi ne da Najeriya a matsayin kasa ba da yankin Naija Delta ba, yana mai jaddada cewa Najeriya dunkulalliyar kasa ce da babu wanda ya isa ya raba ta, ciki har da raba albarkatun da ke cikinta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: