Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya bayyana Alhininsa kan mutuwar wasu mutane a sanadiyar kifewar Jirgin ruwa a kauyen Zhigiri na karamar hukumar Shiroro ta Jihar.

Kimanin mutane 7 ne aka bada rahotan cewa sun mutu a sanadiyar kifewar Jirgin su a ruwa lokacin da suke kokarin zuwa kyauyen Dnaweto wani gari da yake gefe da su domin bikin suna.

Kwanaki 3 da faruwar lamarin Gwamna Abubakar Sani Bello, ya damu da halin da mutanen suka tsinci kansu.

Gwamnan ya Jajantawa da Iyalan mutunen da suka rasa rayukan su, tare da rokon Allah ya jikansu da rahama.

Abubakar Sani Bello, ya ce ya lura da cewa aikin ginin Tashar wutar Lantarki ta Zungeru ya tirsasawa mazauna yankunan yin tafiyar ruwa.

Kazalika, ya bukaci hukumar da take lura da cigaban mutanen da aka ginawa Tashar wutar lantarki a kusa da su akan ta samar da kayayyakin da ake bukata irin su rigar ruwa da sauran su domin bawa mutane damar tsallake ruwa ba tare da fargaba ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: