Ba’a tallafawa da kuma karawa sojin Najeriya kwarin guwiwa – Ali Ndume

0 118

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan kasar nan Sanata Muhammad Ali Ndume, yace ba’a tallafawa da kuma karawa sojin kasar nan da kuma wasu masu aikin damara kwarin guwiwa a yakin da sukeyi da yan ta’adda a kasar nan.

Sanatan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ta wayar tarho a jiya.

Ya ce albashi da kuma wasu kudaden alawus da ake baiwa jami’an sojin kasar nan sunyi kadan su karfafi jami’an domin su samu nasarar kakkabe yan ta’adda.

Ndume yace tun lokacin da shugaban kasa ya shaidawa manyan hafsoshin tsaron kasar nan cewa baya son yaga gazawar su, ya kamata a inganta duk wata walwalar su musamman ma jami’an da suke yaki da yan ta’adda a yankin Arewa maso gabas. Ya bukaci shugaban kasa da ya kara duba lamarin su, ya kuma samar musu isassun kudade da kayan aiki da kuma kara yawan albashin su da kuma kudaden alawus domin samun nasarar shawo kan matsalar tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: