Babban bankin kasa (CBN) yace ya raba sama da naira tiriliyan 1 da miliyan 300,000 domin tallafawa a samar da wutar lantarki a Najeriya cikin shekaru 5 da suka gabata

0 76

Babban bankin kasa (CBN) yace ya raba sama da naira tiriliyan 1 da miliyan dubu 300 domin tallafawa samar da wutar lantarki ga ‘yan Najeriya cikin shekaru 5 da suka gabata.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, shine ya sanar da haka a jiya wajen taron manema labarai biyo bayan wata ganawa da kwamitin masu harkar bankuna a Abuja.

Emefiele yace bankin ya bada naira miliyan dubu 11 da miliyan 110 ga masu ruwa da tsaki a bangaren wutar lantarki a ka0    rkashin shirin kasuwancin wutar lantarki.

Sai dai, Emefiele ya sha alwashin jajircewar bankin wajen cigaba da tallafawa kamfanonin rarraba wutar lantarki domin samar da tsayayyar wutar lantarki ga ‘yan Najeriya.

Emefiele ya kuma ce bankin na CBN zai fara bayar da tallafi ga kamfanin mai na kasa NNPC da nufin tabbatar da cewa ya shigo da albarkatun man da zai kawo karshen karancinsu a kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: