Wani kamfanin sufurin jiragen saman a kasar China dauke da mutane 132 sun fado cikin tsaunuka

0 80

Wani kamfanin sufurin jiragen saman a kasar China dauke da mutane 132 sun fado cikin tsaunuka.

Hukumar kula da sufurin jiragen saman kasar ne ya sanar da aukuwar hadarin a yau da rana cikin wata sanarwa da ta wallafa a internet.

Jirgin kirar Boeing na kan hanyarsa ta zuwa wani birnin a yankin kudu maso yammacin kasar lokacin da ya fadi.

Akwai fasinjoji 123 da masu aikin jirgi 9 a cikin jirgin saman.

Masu aikin ceto sun je wajen da hadarin ya auku amma har yanzu ba a san adadin wadanda suka mutu ko suka samu rauni ba.

Wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan internet sun nuna hayaki na tashi daga wajen da jirgin ya fadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: