Gwamnatin Jihar Kaduna ta ayyana dokar ta baci tsawon awanni 24 a kananan hukumomin Jema’a da Kaura na jihar

0 24

Gwamnatin Jihar Kaduna a yau ta ayyana dokar ta baci tsawon awanni 24 a kananan hukumomin Jema’a da Kaura na jihar.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gid ana jihar, Samuel Aruwan, ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Kaduna.

Samuel Aruwan yace biyo bayan shawarwarin daga hukumomin tsaro, gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana dokar hana fita kwata-kwata a kananan hukumomin Jema’a da Kaura na jihar ba tare da bata lokaci ba.

Ya kara da cewa an bawa hukumomin tsaro damar tabbatar da dokar.

Kwamishinan yace za a sanar da Karin bayani idan an samu bukatar hakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: