Akalla mutane 5 aka kashe yayin da wasu da dama suka jikkata a mummuna rikicin da ya auku tsakanin manoma da makiyaya a yankin karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa.

An rawaito cewa gomman mutane sun jikkata a rikicin, wanda aka ce ya auku ne sanadiyyar rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu.

A cewar wani ganau, lamarin da auku a ranar kasuwar mako ya jawo mutuwar wani mutum guda, inda ya haifar da harin ramuwar gayya.

Ana yawan samun rikici a kananan hukumomin Guri, Kirikasamma da Birniwa tsakanin manoma da makiyaya.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan jihar Jigawa, Lawan Shiisu Adama, yace Fulani makiyaya da manoma sun yi rikici a dajin Magirami dake karamar hukumar Guri, inda ya kara da cewa tuni jami’an yansanda karkashin jagorancin DPO na Guri suka ziyarci wajen domin wanzar da zaman lafiya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: