Babban jami’in dan sanda Abba Kyari ya musunta tuhumar da ake masa, yace bai aikata laifin safarar hodar Ibilis ba

0 115

Babban jami’in dan sanda Abba Kyari wanda hukumar NDLEA ke tuhuma da safarar hodar ibilis a wata shari’ar da ta gurfanar da shi a wata babbar kotun da ke Abuja ya musanta cewa ya aikata laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Hukumar hana tu’ammali da miyagu kwayoyi ta NDLEA ce ta gurfanar da Abba Kyari da wasu mutum shida a kotun.

Sauran mutanen da ake tuhumar su da aikata laifin tare da Abba Kyari sun hada da Sunday J. Ubua, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da Bawa James, mataimakin sufritandan ‘yan sanda da Simon Agirgba da kuma John Nuhu wadanda dukansu sufetan ‘yan sanda ne.

Sauran mutanen sun hada da Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne.

Hukumar NDLEA ta ce Abba Kyari da wasu jami’an da ke tamaka masa sun yi awo gaba da kilo 21.25 na koken, hodar Iblis din da suka kwace a hannun wasu masu safarar ta, kuma hukumar ta ce abin da suka aikata laifi ne.

A yau Litinin ne aka fara wannan shari’ar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: