Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi watsi da ikirarin da yan adawa keyi akan cewa jam’iyyar APC zata rushe

0 59

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayi watsi da ikirarin da yan adawa keyi akan cewa jam’iyyar APC zata rushe gabanin ko bayan babban taron ta na kasa da za’agudanar a ranar 26 ga watan nan na Maris, tare da tabbatar da cewa zasu bawa yan adawa mamaki.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin dayake amsa tambayoyin manema labaran fadar shugaban kasa a filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe dake babban birnin tarayya Abuja.

Kafin hakan dai shugaban kasar yayi niyyar zuwa London ne daga birnin Nairobi na kasar Kenya, bayan kammala taron majalissar dinkin duniya na muhalli karo 50.

Sai kuma shugaban ya fasa ya kuma dawo Nigeria a ranar Juma’a.

A cewar shugaba Buhari tafiyar zuwa birnin London bazai dakatar da komai ba a kasar nan, kasancewar ya mika ragamar komai ga mataiamakin shugaban kasa, wanda zaiyi aiki tare da sakataren gwamnatin tarayya da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugbaan kasa.

Idan zamu iya tinawa dai a ranar 1 ga wannan watan Maris na wannan shekara, mai Magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina yace shugaban zaije London ne domin a duba lafiyar sa, kuma zai shafe makonni kafin ya dawo kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: