Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kuduri na yin Allah wadai da Rasha kan mamayar da ta yi wa Ukraine

0 75

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a jiya ya amince da wani kuduri na yin Allah wadai da Rasha kan mamayar da ta yi wa Ukraine tare da neman janyewar kasar cikin gaggawa.

Kuri’ar dai ta samu amincewar kasashe 141, biyar suka ki amincewa, 35 kuma suka ki kada kuri’a.

A makon da ya gabata ne Rasha ta ki amincewa da daftarin kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya yi Allah wadai da mamayar da ta yi wa Ukraine.

A rana ta bakwai da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, ana sa ran kasashen biyu za su cigaba da tattaunawa yau a Belarus.

An kawo karshen tattaunawar farko a ranar Litinin ba tare da cimma wata matsaya ba.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Ukraine a jiya ta ce sama da fararen hula dubu 2 ne aka kashe tun bayan fara mamayar a ranar Alhamis da ta gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: