Babbar jam’iyyar adawa ta Turkiyya ta yi iƙirarin samun manyan nasarori a zaɓen da aka yi

0 122

Babbar jam’iyyar adawa ta Turkiyya ta yi iƙirarin samun manyan nasarori a zaɓen da aka yi cikin manyan biranen ƙasar na Istanbul da Ankara.

Sakamakon wata babbar mahangurɓa ce ga Shugaba Recep Tayyip Erdogan, wanda ya yi fatan sake karɓe iko da biranen, ƙasa da shekara ɗaya bayan ya yi nasarar zama shugaban ƙasa a wa’adi na uku.

Ya dai jagoranci yaƙin neman zaɓe a birnin Istanbul, inda ya girma har ya zama magajin gari.

Sai dai Ekrem Imamoglu, wanda ya yi nasarar cin zaɓen magajin birnin karon farko a 2019, ya samu nasara a karo na biyu da jam’iyyarsa ta adawa wadda babu ruwanta da wani tsarin addini ta CHP. Shugaba Erdogan dai ya yi alƙawarin buɗe sabon shafi a ƙasaitaccen birnin mai yawan jama’a kusan miliyan 16, sai dai magajin birnin Istanbul mai ci yana gab da samun fiye da kashi 50% na ƙuri’un da aka kaɗa, inda zai kayar da ɗan takarar jam’iyyar AP ta shugaba Erdogan da maki fiye da 11 da kuma ƙuri’u kusan miliyan ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: