Babbar Magana: Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Soke Zaɓen Dino Melaye

0 248

A ranar Juma’a ne Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke zaɓen Sanata Dino Melaye, sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a Majalisar Dattijai.

“Yanzu-yanzu nayi rashin nasara a Kotun Ɗaukaka Ƙara, kuma kotun ta bada umarnin sake sabon zaɓe”, ya rubuta haka ranar Juma’a a shafinsa na Twitter.

A ranar Juma’a, 23 ga Agusta, Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta soke zaɓen Dino Melaye.

Bayan soke zaɓen nasa ne, sai Mista Melaye ya garzaya zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara don ƙalubalantar hukuncin, inda ita ma yau ta tabbatar da hukuncin kotun farko.Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta bayyana Mista Melaye, ɗan takarar jam’iyyar PDP, a matsayin wanda ya lashe zaɓen 23 ga Fabrairu.

Ɗan takarar jam’iyyar APC, Smart Adeyemi ne ya ƙalubalanci nasarar Mista Melaye a kotu.Mista Adeyemi ya ƙalubalanci nasarar Mista a bisa dalilai uku, rashin bin ƙa’ida, aringizon ƙuri’u da rashin bin dokar zaɓe.

Gungun alƙalai uku, bisa jagorancin Mai Shari’a A. O Chijioke a wani hukunci da gaba ɗaya suka amince da shi sun umarci INEC da ta sake zaɓe.Duk da wannan hukunci na kotu, Mista Melaye ya ce: “A dukkan abubuwa, na kan gode wa Allah”.

Ya ci gaba da cewa: “Duk wanda ya fara wani abu mai kyau, tabbas zai ƙarasa shi.Ya bayyana ƙarfin gwiwarsa na lashe zaɓen da kotu ta ce a sake, kuma ya yi kira ga magoya bayansa da su zama masu kiyaye doka, yana mai lura da cewa shi da magoya bayansa “a koyaushe za su yi nasara”.

Leave a Reply

%d bloggers like this: