Bamu damu da goyon bayan da wasu gwamnonin APC suke nuna wa Tinubu ba – Babachir Lawan

0 160

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya ce goyon bayan da wasu gwamnonin APC suka nuna wa Shugaba Bola Tinubu domin ya sake tsayawa takara a 2027 bai dame su ba.

Ya ce su a cikin ƙungiyarsu ta masu haɗaka sun fi mayar da hankali ne kan talakawa, ba shugabanni ba.

“acewarsa ko da dukkanin gwamnonin jihohi 36 da Abuja sun koma APC, babu abin da zai canja.

Ƙungiyar masu haɗaka ƙarƙashin jagorancin Atiku Abubakar, Peter Obi, da Nasir El-Rufai ta zaɓi jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyyar da za su kara da APC a zaɓen 2027.

Ya kara da cewa suna da ƙwarewa kuma muna aiki a hankali, a lokacin da ya dace, za su bayyana wa duniya shirinsu,”.

Leave a Reply